Syria-Turkiya

'Yan tawayen Kurdawa sun fara barin iyakar Syria da Turkiya

Wasu 'yan tawayen Kurdawa da suka fara barin yankunansu karkashin yarjejeniyarsu da Turkiya.
Wasu 'yan tawayen Kurdawa da suka fara barin yankunansu karkashin yarjejeniyarsu da Turkiya. Delil SOULEIMAN / AFP

'Yan Tawayen Kurdawan da ke Tal Abyad na arewacin Syria sun fice daga birnin sakamakon kawanyar da dakarun Turkiya suka musu kafin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla.

Talla

Yarjejeniyar da Amurka ta jagoranta ya baiwa Kurdawan zuwa gobe talata su fice daga Yankin ko kuma Turkiya ta sake kaddamar da hare hare.

kwamandan Kurdawa Mazloum Abdi ya ce za su janye zuwa kilomita 120, yayinda Turkiya ta ce tana bukatar su janye zuwa kilomita 440 daga iyakar ta.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ya ga manyan motoci akalla 50 tare da motocin daukar marasa lafiya na barin garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.