Barazanar Dumamar yanayi ta zarta ta nukiya a duniya- Santos

Tsohon shugaban Colombia Juan Manuel Santos, ya ce a halin da ake ciki, barazanar da matsalar sauyin yanayi ke yiwa duniya, ta zarta ta yaki da makaman nukiliya. Santos ya yi gargadin ne, a lokacin da yake jawabi ga taron masu ruwa da tsaki na duniya kan muhalli da aka kammala a birnin Dubai.

Tsohon shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos.
Tsohon shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos. REUTERS/Carlos Julio Martinez
Talla

Tsohon shugaban na Clombia ya ce bayan kawo karshen yakin duniya na 2, barazanar amfani da makaman nukiliya wajen yaki ita ce matsala mafi girma da dan adam ke fuskanta, sai dai a halin yanzu matsalar dumama ko sauyin yanayi ke dauke da barazana mafi girma, matsalar makaman kare dangin na nan kwance.

Yayin taron na kwanaki 2, kwararru, sun bukaci gaggauta aiwatar da tsare-tsaren yarjejeniyar yaki da matsalar dumamar yanayi da aka cimma a Paris cikin 2015, musamman ta fannonin, rage fitar da gurbatacciyar Iskar Carbon, da kakaba haraji kan fitar da ita, sai kuma samarwa da saukaka amfani da makamashin da ake sabuntawa.

Cikin watan Oktoban nan, asusun bada lamuni na duniya IMF ya bukaci manyan kasashen dake kan gaba wajen fitar da iskar carbon, su amince da biyan harajin dala 75 kan duk ton guda na gurbatacciyar Iskar da suke fitarwa har na tsawon shekaru 10, inda za a rika amfani da harajin wajen kyautata muhalli da dazuka da kuma karfafa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa.

Muna Mika sakon ta’azziya ga Iyalan Malam Musa Soba, wanda A yayi wa rasuwa yau litinin a garin Tudun Saibu dake karamar hukumar Soba, Kaduna. Da fatan Allah ya jikanshi da Rahama Ameen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI