Isa ga babban shafi
Kasuwanci

China da India na sahun kasashe 10 masu saukaka kasuwanci

习近平和莫迪4月28日在武汉东湖乘船游览喝茶交谈
习近平和莫迪4月28日在武汉东湖乘船游览喝茶交谈 路透社
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
2 Minti

Bankin duniya ya sanya sunayen kasashen China da India a sahun farko na jerin kasashen da gwamnatocinsu ke saukaka harkokin kasuwanci cikin shekarun baya-bayan nan ga al’ummomin kasashe.

Talla

Cikin rahoton da bankin na duniya ya fitar kan kasashen ‘yan gaba gaba wajen saukaka harkokin kasuwanci ga al’ummarsu, bankin ya ce duk da rikicin kasuwancin da ke ciwa China tuwo a kwarya hakan bai hana ta zamowa cikin jerin ‘yan goman farko da ke fafutukar saukaka kasuwanci a kasashensu ba.

China wadda ke matsayin ta 4 wannan ce shekara ta 2 a jere da take shiga sahun ‘yan goman farko yayin da India wadda ke matsayin ta 7 cikin shekara ta 3 a jere da take samun wannan tagomashi, sun bar Faransa a baya wadda yanzu ta dawo matsayin ta 15 maimakon ta 35 da take a baya.

A cewar David Malpass shugaban bankin na duniya kasashen China da India sun samar da sauye-sauyen haraji baya ga dokokin shige da fice da suka saukaka harkokin cinikayya duk da kalubalen da kasuwanci ke fuskanta a halin yanzu.

Bankin wanda ya gudanar da binciken kan yadda kasashen ke bayar da damar kasuwanci ya ce duk da yakin kasuwancin da Chinar ke fuskar bai hana ta samar da sabbin tsare-tsaren da suka saukakawa ‘yan kasuwar gudanar da harkokinsu ba.

Sauran kasashen da bankin duniyar ya bayyana a masu saukaka harkokin kasuwanci akwai New Zealand a matsayin ta 1 sannan Singapore tukuna Hong Kong kana Korea a matsayin ta 5 da kuma Amurka a matsayin ta 6.

Sauran kasashen da bangaren kasuwancinsu ya habaka tattalin arzikinsu akwai Saudiya Arabia kana Jordan sai Togo da Bahrain sannan Tajikistan kana Pakistan sai Kuwait da kuma India sannan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.