Syria

Martanin shugabannin kasashe kan mutuwar al-Baghdadi

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da yin tsokaci kan mutuwar jagoran kungiyar IS Abubakar al-Baghdadi, a wani farmaki sirri da dakarun Amurka suka kaiwa maboyarsa a arewa maso yammacin Syria.

Abu Bakr al-Baghdadi.
Abu Bakr al-Baghdadi. Reprodução/Le Point
Talla

Ranar lahadin nan 27 ga Oktoban 2019, Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da mutuwar al-Baghdadi, inda ya ce jagoran na IS ya yi mutuwa irin ta kare, bayan da ya kashe kansa ta hanyar tarwatsa damarar bam din jikinsa.

Trump ya ce an samu nasarar ce da taimakon kasashen Rasha, Syria, Turkiya da kuma Iraqi.

Sai dai a sakon da ya aike, fira ministan Birtaniya Boris Johnson yayi gargadin cewa duk da cewa mutuwar al-Baghdadi babbar nasara ce, hakan baya nufin kawo karshen kungiyar ta IS. Shi ma Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, bayyana mutuwar jagoran na IS yayi a matsayin babbar nasara kan yakin da za a shafe tsawon lokaci ana fafatawa da ta’addanci.

A bangaren Faransa kuwa, ministan tsaron kasar, Florence Parly alhini da sakon taya jimami ta aike ga wadanda ayyukan ta’addancin da al-Baghdadi ya jagoranta suka rutsa da su.

Shi kuwa kakin ma’aikatar tsaron Rasha Igor Konashenov, gargadi yayi kan cewar kada a dauki mutuwar al-Baghdadi a matsayin wani abin tasiri kan kyautatuwar tsaro a Syria da sauran makwabtan yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI