Amurka

Amurka ta binne gawar jagoran IS a cikin teku

Wani babban jami’in Ma’aikatar Tsaron Amurka ya ce, an nutsar gawar jagoran kungiyar Daesh ko kuma IS Abu Bakr al-Baghdadi a teku bayan da dakarun kasar ta Amurka suka kai harin da ya yi sanadiyar mutuwarsa a Syria.

Abu Bakr al-Baghdadi.
Abu Bakr al-Baghdadi. © AFP
Talla

Jami’in na Amurka bai yi karin bayani dangane da rana, lokaci ko kuma inda aka nutsar da gawar al-Baghdadi ba, to sai dai sanarwar na tunatar da duniya irin salon da Amurkan ta yi amfani da shi wajen batar da gawar jagoran Alqa’ida Osama bin Ladan a 2011.

Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Mark Esper ya ce, mutuwar al-Baghdadi na a matsayin gagarumin koma-baya ga sauran mambobin kungiyar IS da ke ikirarin jihadi.

Espaer ya jinjina wa kusan dakarun Amurka 100 da suka yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen far wa jagoran ‘yan ta’addan a maboyarsa da ke yankin Idlib na Syria.

Mayakan Kurdawa sun yi ikirarin cewa, su ne kashin-bayan basirar da ta kai ga nuna wa Amurka maboyar al-Baghdadi wanda aka shafe shekaru da dama ana nema ruwa a jallo sakamakon ta'asar da ya aikata a duniyar ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI