Macron na ziyarar huldar kasuwanci a China
Wallafawa ranar:
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyara a China domin kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci, a daidai lokacin da masu masaukinsa ke gargadin sa da ya kauce wa batutuwan da suka shafi rikicin Hong Kong.
Ana sa ran Macron ya halarci bikin baje kolin kasashen duniya a Shanghai, kafin a masa liyafar cin abincin dare.
Daga nan shugaba Macron da mai masaukinsa Xi Jinping za su koma birnin Beijing, inda za su gudanar da tattaunawa a tsakaninsu.
Kungiyar Human Rights Watch ta bukaci Macron da ya yi matsa wa shugaba Xi don ganin ya rufe sansanonin “ilimin siyasa” da ke Xinjiang tare kuma da mutunta ‘yancin al’ummar Hong Kong na shiga cikin siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu