Iran-Turai

Kalubalen ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran yana karuwa - EU

Cibiyar inganta makamashin Uranium ta Bushehr dake kudancin Teheran, babban birnin kasar Iran.
Cibiyar inganta makamashin Uranium ta Bushehr dake kudancin Teheran, babban birnin kasar Iran. REUTERS/Raheb Homavandi

Kungiyar kasashen Turai EU ta bayyana damuwa kan sanarwar da Iran ta fitar a yau talata, na shirin ci gaba da aikin tacewa da kuma inganta makamashin Uranium a wata cibiyar karkashin kasa dake kudancin kasar, abin da ka iya bata damar mallakar makaman kare dangi.

Talla

Jim kadan bayan sanarwar ta Iran, Kakakin kungiyar EU Maja Kocijancic ta bayyana damuwa kan karuwar kalubalen da tace suna fuskanta wajen ceton yarjejeniyar nukiliyar da suka cimma da Iran a 2015 daga rushewa, wadda a watan Mayun bara, Amurka ta fice daga cikinta.

Bayan janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar ce kuma, shugaban Amurkan Donald Trump ya sake laftawa Iran din jerin takunkuman karya tattalin arzikin da tsohon shugaba Barrack Obama ya janye, matakin da ya fusata kasar ta Iran, ta kuma soma bijirewa wasu sassan yarjejeniyar takaita shirin nukiliyar data cimma da manyan kasashen Turan.

Tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar kasashen Faransa, Jamus da Birtaniya da kungiyar Eu suka soma kokarin ceto ta, sai dai har yanzu Iran bata gamsu da kokarin na su ba, la’akari da gaza soma aiki ko tasirin shirin samar da kafa ga kamfanonin Turai don ci gaba da hulda da Iran duk da takunkuman da Amurka ta kakaba mata.

A farkon makon gobe ake sa ran ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen Turai EU za su yi taro a Birnin Brussels, inda za su tattauna kan batun nukiliyar Iran din da sauran lamurran Yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI