Faransa-China

Macron ya kulla yarjejeniyar Kasuwanci da China

Shugaban Faransa a China
Shugaban Faransa a China Fuente: Reuters.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanya hannu kan yarjeniyoyin kasuwanci da dama tare da mai masaukin sa shugaban China Xi Jinping a cigaba da ziyarar kasar China.

Talla

Bayan halartar bikin baje kolin Shanghai da kuma tattaunawa daban daban, yau ake saran shugaba Emmanuel Macron tare da mai masaukin sa shugaban China Xi Jinping su sanya hannu kan yarjeniyoyin kasuwanci.

A jiya talata, shugaba Macron yay aba da yadda shirin al’adu ke hada kan mutanen kasashen biyu, lokacin da yake kaddamar da Cibiyar Al’adu ta Pompidou a Shanghai wanda shine irin sa an farko a wajen Turai.

Cibiyar da wani Baturen Ingila ya zana aka kuma gina a gabar ruwan Huangpu da ya ratsa birnin mai mutane miliyan 24 na da tarin kayan tarihi 25,000 da kuma dakunan tarurruka.

Shugaba Macron ya kwashe sa’a guda a Cibiyar yana zagayawa tare da uwargidan sa Briget da shugabannin kula da al’adun kasar cikin su harda mawaki Jean Michel Jarre da mai zane zane Yan Pei-Ming.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.