Amurka

Majaliar Amurka na fatan sauraren wani makusancin Trump

Shugaban Ukrain  Volodymyr Zelenskiy  lokacin ya ziyarci Amurka
Shugaban Ukrain Volodymyr Zelenskiy lokacin ya ziyarci Amurka REUTERS/Gleb Garanich

Majalisar Wakilan Amurka dake yunkurin tsige shugaba Donald Trump ta aike da sammaci ga Babban Hafsa a fadar shugaban kasa, Mick Mulvaney domin gurfana a gaban ta, ya bada ba’asi kan yunkurin Trump na tirsasawa shugaban Ukraine.

Talla

Shugaban kwamitoci 3 dake bincike shugaba Trump yace binciken da suke gudanarwa ya nuna musu cewar akwai alamun jami’in na da hannu wajen ingiza shugaban da wakilin sa Rudolph Giuliani da kuma wasu mutane wajen hana bada taimakon tsaro na kusan Dala miliyan 400 ga Ukraine har sai ya amince ya biyawa Trump bukatun san a siyasa.

Yanzu haka dai Mulvaney ne jami’i mafi girma da kwamitin ya gayyata domin gurfana a gaban sa ranar juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI