NATO

NATO na shure-shuren mutuwa- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, kungiyar tsaro ta NATO na shure-shuren mutuwa, lura da matsalar rashin fahimtar juna da ke tsakanin Amurka da sauran kasashen Turai, da kuma yadda Turkiya ta yi gaban kanta wajen kaddamar da farmaki a Syria.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Shugaba Macron ya bayyana haka ne a yayin wata zantawa da Mujallar Economist, inda yake cewa babu kyakkyawan tsarin cimma matsaya tsakanin Amurka da sauran kasashe mambobin NATO.

Shugaban ya koka kan yadda Turkiya wadda ta kasance mamba a NATO, ta dauki tsattsauran mataki a Syria , kasar da ya ce, manufofinsu a cikinta na fuskantar barazana.

Kakkausan kalaman Macron dai, sun diga ayar tambaya ne dangane da makomar wannan Kungiya ta NATO wadda ke shirin gudanar da taronta nan da watan gobe a Birtaniya.

Shugaban ya kara da cewa, dole a matsayinsu na mambobin NATO, su amince cewa, lalle suna fama da tarin matsaloli, yayin da ya yi gargadi kan yadda Amurka ke karan-tsaye ga lamurran kungiyar.

Tuni gwamnatin Rasha ta yi jinjina ga kalaman Macron, inda ta kwatanta kalaman nasa da gwala-gwalai.

Sai dai Shugabar Gwmantin Jamus, Angela Merkel ta yi watsi da kalaman na Macron, tana mai cewa, babu bukatar yanke wa kungiyar irin wannan hukunci na gaggawa ko da kuwa tana fama da matsaloli.

Shugaban kungiyar NATO, Jens Stoltenberg ya jaddaa cewa, har yanzu kungiyar nada karsashinta, sannan kuma Amurka da kasashen Turai na aiki tare fiye da yadda aka sani a can baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI