Iraq

Akala mutane 300 ne suka mutu a Iraqi tun bayan barkewar zanga-zanga

Zanga-zanga a kasar Iraqi
Zanga-zanga a kasar Iraqi REUTERS/Saba Kareem

A Iraqi , Gwamnatin kasar ta tsaya kan bakar ta na ci gaba da kaucewa bukatar masu zanga-zanga.An samu tashin hankali a wasu yankunan kasar, inda aka bayyana mutuwar wasu daga cikin yan kasar.Akala mutane 300 ne suka rasa rayukan su a zanga-zangar kasar ta Iraqi.

Talla

Duban yan kasar ne suka sake fitowa a yau juma’a, mako na uku biyo bayan zanga-zangar farko ta nuna kyamar gwamnatin Iraqi.

A jiya Alhamis akalla mutane 13 aka tabbatar da mutuwar su, shida a Bagdaza, wasu mutane 7 a garin Bassora dake kudancin kasar, yayinda wani rahoto daga bangaren asibitoci ya bayyana salwantar rayukan mutane 300 tun bayan da wanan zanga-zanga ta kuno kai a farkon watan Oktoban da ya shude.

Firaministan kasar da ya bayyana fatan sa na sauka daga mukaminsa a farkon watan Oktoban, na ci gaba da aikewa da sanarwo’I na gayyatar yan kasar ga zaman lafiya, yayinda masu zanga-zanga ke ci gaba da neman Shugaban kasar yayi murabis.

A wasu sassan kasar masu boren sun dace hanyoyin dake bayar da dama na zuwa tashoshin tasho man fetur,kazantar zanga-zangar ta hadasa cukoson manyan motocin dakon mai dake dauke da kusan gangar mai dubu 100 a kan hanyar zuwa kasuwar Duniya daga arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.