Bolivia

'Yar Majalisar Dattijai Ta Sanar Da Hawa Shugabancin Bolivia

Tsohon shugaban Bolivia Evo Morales
Tsohon shugaban Bolivia Evo Morales RFI

Wakiliya a Majalisar Dattawan Bolivia ta sanar da itace sabuwar shugaban kasar bayan da Evo Morales ya ajiye shugabancin ya tsere zuwa Mexico don samun mafakar siyasa.

Talla

Jeanine Anes daga bangaren adawa ta sanar da cewa ita take kan layi a jerin masu hawa kujeran kuma za ta ci gaba da tafiyar da mulkin kasar.

Sai dai kuma wakilan jam'iyar tsohon shugaba Evo Morales sun kauracewa zaman majalisar wanda hakan ya sa babu adadin yawan wakilai da suka dace su zauna su yi aikin majalisar.

Shi kansa tsohon shugaba Evo Morales ya soki nadin da wakilar majalisar Dattawan ta yi cewa itace sabuwar shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.