Amurka-Trump

Majalisa ta fara sauraron shaidu kan shirin tsige Trump

Shugaba Donald Trump na
Shugaba Donald Trump na rfi

An fara sauraro a bainar jama’a,a  Laraban nan, bahasi kan shirin tsige shugaban Amurka Donald Trump, inda ake karbar  bayanai da za su iya kaiwa ga tsige shi.

Talla

Bayanai na nuna fara sauraron zarge-zargen a bainar jama'a da ake yiwa Trump kai tsaye ta kafofin Talabijin ake nunawa duniya.

Wannan al’amari na daga cikin manyan kalubalen dake fuskantar Shugaba Trump a tsawon shekaru uku da yayi bisa madafun iko yanzu haka.

Sama da wata guda kenan ana ta daukan matakan ganin an tsige Donald Trump.

Bayan zaman a bainin jama'a ne wakilan majalisar Dattawa za su jefa kuri'ar amincewa da matakin da aka dauka kafin zartasda tsige shi.

Manyan zarge-zargen da ake yi wa Trump kan fito ne daga wasu bayanan sirri da ake samu na kauce hanya wajen mulkin da yake yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI