Amurka

Amurka za ta ci gaba da yakar kungiyar IS - Pompeo

U.S. Secretary of State Mike Pompeo speaks to reporters in the briefing room of the White House in Washington, U.S., September 10, 2019.
U.S. Secretary of State Mike Pompeo speaks to reporters in the briefing room of the White House in Washington, U.S., September 10, 2019. REUTERS/Kevin Lamarque

Sakataren Waje na Amurka Mike Pompeo ya baiwa kasashen kawance dake yakar kungiyar IS cewa Amurka za ta ci gaba da wannan yaki , said ai kuma akwai bukatar dukkan kasashen da su bada tasu gudunmawa.Mike Pompeo na Magana ne a taro na musamman a Washington dake samun halarcin kasashen duniya 30, wanda Faransa ta nemi a yi don tattauna yadda za’a tunkari yakar ‘yan kungiyar ta IS.

Talla

Yau gashi mung a bayan kungiyar IS, wammam ne ma yasa muke ci gaba da kasancewarmu a kudancin Syria inda muna iya kai hare-hare ta sama.

Mun kuma kara girke dakarunmu a arewa maso gabashin Syria, da sauran sassan kasar. Duk dai domin mu kara takurawa ‘yan kungiyar IS ta yadda ba zasu sake samun sakat ba balle har su sake kama filayen mai.

Dole ne kawayenmu su karbi dubban mayaka na kasashen duniya da suka kai agaji, kuma aga lallai an dora masu alhakin laifukan da suka aikata.

Mun sami tabbaci daga kawayenmu dake kasa, cewa za su ci gaba da ganin ba’a. yi sake ba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.