Amurka

Zan bayar da shaida kan yunkurin tsige ni-Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka Zach Gibson / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta bayyana a gaban Majalisar Dokokin Kasar domin bayar da shaida kan binciken yunkurin tsige shi daga karagar mulki, inda ya ce, yana matukar duba yiwuwar karbar kalubalen da ya kunno kai daga bangaren jam’iyyar adawa ta Democrat.

Talla

Bayan da shugabar Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta bude wa Trump kofa domin fadin gaskiyarsa, shugaban ya ce, yana zumudin yin haka.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Trump ya ce, Pelosi ta bukaci na bayar da shaida kan yunkurin tsige ni na bita da kulli, kuma ta ce, zan iya bayar da shaidar a rubuce.

Trump ya ce, ya yi madalla da wannan batu, kuma yana duba yiwuwar karbar sa domin bai wa Majalisar Dokokin Amurka damar ci gaba da gudanar da ayyukanta.

Sai dai kawo yanzu, babu cikakken bayani kan irin shaidar da shugaban ya kudurci bayar da ita, yayin da ake ganin cewa, babu makawa, tawagar da ke ba shi kariya a binciken, za ta ki amince wa da batun bayyanarsa a gaban Kwamitin Bayanan Sirri na Majalisar Wakilan Amurka da ke bincike kan zargin Trump da ya yi wa takwaransa na Ukraine matsin lamba don ganin ya bata sunan babban mai hamayya da shi, wato Joe Biden da zummar kara masa tagomashin sake zabensa a 2020.

A bangare guda wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da gidan talabijin din ABC ya gudanar, ya nuna cewar sama da rabin Amurkawa na goyan bayan tsige shugaba Trump saboda karya ka’idar da ya yi wajen hulda da Ukraine.

Sakamakon jin ra’ayin jama’ar ya nuna cewar kashi 51 na Amurkawa na bukatar a  gurfanar da Trump a kotu bayan tsige shi domin fuskantar hukunci, yayin da kashi 6 suka bukaci tsige shi ba tare da hukunta shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI