Tarayyar Turai-Amurka

EU ta yi tur da Amurka kan gine-ginen Isra'ila a yankin Falasdinu

Wasu daga cikin gidajen da Isra'ila ta gina a yankunan Falasdinawan data mamaye a Yamma da kogin Jordan.
Wasu daga cikin gidajen da Isra'ila ta gina a yankunan Falasdinawan data mamaye a Yamma da kogin Jordan. Reuters

Karon farko cikin tsawon shekaru 40, Amurka ta sauya matsayinta kan gine-ginen kama wuri zauna da Isra'ila ke yi a sassan yankunan Falasdinawa, wadanda a yanzu Amurkan ta ce halastattu ne, sabanin yadda a baya ta haramta gine-ginen.

Talla

Wannan ce tasa kungiyar kasashen Turai EU ta bayyana takaicinta kan sabon matsayin na Amurka.

Kasashen kungiyar ta EU sun yi tur da Amurkan ne jim kadan bayanda sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo yace sun sauya matsayinsu kan gine-ginen, inda yace daga yanzu basa kallonsu a matsayin haramtattu.

Babbar jami’ar diflomasiyar Turai, Federico Mogherini tace matsayin kungiyar su bai sauya ba, kan cewa duk wani gini da Israila tayi a yankunan Falasdinawa haramtacce ne kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Ita ma dai kungiyar Falasdinu tayi watsi da matsayin na Amurka, yayinda Israila ta bayyana farin cikinta da sabon matsayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.