Hakkin Mata

Mata 137 ake yiwa kisan gilla kowace rana a sassan duniya - MDD

Wasu daga cikin mata sama da dubu 1 da 200 da suka yi zanga-zanga a Paris, kan yawaitar yiwa mata kisan gilla da makusantansu ke yi da gangan.
Wasu daga cikin mata sama da dubu 1 da 200 da suka yi zanga-zanga a Paris, kan yawaitar yiwa mata kisan gilla da makusantansu ke yi da gangan. AFP

Wata sabuwar kididdigar majalisar dinkin duniya ta nuna cewar, mata akalla 137 makusantansu ke yiwa kisan gilla da gangan kowace rana a sassan duniya, cikin shekarar 2017.

Talla

Rahoton na ofishin majalisar dinkin duniya mai sa ido kan yakar manyan laifuka da tu’ammuli da miyagun kwayoyi, ya ce a shekarar ta 2017 kadai, mata manya da kanana akalla dubu 87,000 makusantansu ko dangi suka kashe a sassan duniya.

Rahoton ya ce kashi 58 cikin 100 na jimillar matan da aka halaka, wani shakiki daga iyalinsu ne, miji, ko kuma farka ya kashe su, inda binciken ya kara da cewar cikin jimillar matan dubu 87, dubu 30 mijinsu ne ko farka yayi musu kisan gillar, yayinda dubu 20 suka halaka a hannun wani daga cikin ‘yan uwansu na jini da suka hada da Kawu, Yaya, ko kuma mahaifi.

Majalisar dinkin duniyar ta ce a jimlace mata sun fi fuskantar barazanar kisa a nahiyar Afrika daga mazajensu ko ‘yan uwa na jini da kashi 70, idan aka kwatanta da nahiyar Turai inda kashi 38 na matan ke cikin wannan kangi.

Dangane da kasashen da aka fi yiwa mata kisan gillar kuwa da, El Salvador ke kan gaba da kashi 13.9 cikin kowane adadin matan dubu 100 a 2017, Jamaica ke biye da ita da kashi 11, sai kuma Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da aka halaka kashi 10.4 na adadin matan dubu 100, yayinda Afrika ta Kudu aka halaka kashi 9.1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI