Lebanon

Masu zanga-zanga na zargin Gwamnatin Lebanon da assasa rashawa

Masu zanga-zanga a Lebanon
Masu zanga-zanga a Lebanon REUTERS/Aziz Taher

Yau kasar Lebanon ke cika shekaru 76 da samun ‘yancin kai, sai dai masu zanga zanga a kasar sun ce yanzu suka kama hanyar samun ‘yancin kai na hakika.Wannan shine karo na farko da masu zanga zangar daga bangarorin siyasa da addinai daban daban suka hada kan su domin kalubalantar shugabannin siyasar kasar dangane da cin hanci da rashin shugabanci na gari.

Talla

A ranar 22 ga watan Nuwambar shekarar 1943 Lebanon ta samu ‘yanci kai bayan kwashe shekaru 23 a karkashin kulawar kasar Faransa, kafin yakin basasar da ya gudana tsakanin shekarar 1975 zuwa 1990.

Yan watanni da suka gabata Gwamnatin tsohon Firaminista Hariri ta fuskanci barrazana daga masu zanga dake kalon gwamnatin a matsayin wace ta kasa cika alkawuratareda asasa cin hanci da rashawa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.