Trump ya zarta tsohon shugaban kasar Nixon mai Murabus Tabargaza

Shugaban Amurka Donald Trump, yayin wata ganawa da mukarrabansa
Shugaban Amurka Donald Trump, yayin wata ganawa da mukarrabansa REUTERS/Tom Brenner

Shugaban kwamitin binciken tsige shugaban Amurka Donald Trump a majalissar dokokin kasar Adam Schiff, ya bayyana abin da Trump ya aikata tsakanin sa da Ukraine ya fi muni fiye da abin da ya kai ga Murabus din tsohon shugaban Amurka Richard Nixon.

Talla

Shugaban kwamitin binciken ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin da yake takaita bayanai kan batun tsige shugaban na Amurka Donald Trump, bayan kwashe kwanaki kwamitin Majalisar na sauraron shaidu daban-daban, a bainar jama’a kan ko Trump ya yi amfani da karfin ofishinsa ta hanyar tursasawa Ukraine taimaka masa a kokarinsa na sake neman shugabancin Amurka a zabe mai zuwa.

Cikin kwanaki 3 da suka gabata ‘yan majalisun sun saurarari shaidun da suka fi tayar da hankali daga manyan jami’an gwamnatin Trump, tun bayan abin kunyar da ‘Yan Democrat ke zargin sa da aikatawa a wani hira ta wayar tarho da ya yi da takwaransa na Ukraine a ranar 25 ga watan Yulin wannan shekara.

Mista Trump ya dakatar da kusan dala miliyan 400 na taimakon soji, da kuma ziyarar White House don ganawa da sabon shugaban na Ukraine Volodymyr Zelensky, duk domin tilastawa hukumomin taimaka masa.

'Yan majalisun jam'iyyar Democrat dai sun ce da tuni makircin ya yi aiki, ba don bayanan hirar wayar ya iso musu Majalisa cikin kankanin lokaci ba.

Wannan ne ma ya ja hankalin shugaban kwamitin binciken Majalisar kan tsige Trump, Adam Schiff, cewar lamarin ya fi karfin badakalar Watergate na 1972 da ta tilastwa shugaban Amurka na wancan lokaci Richard Nixon yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI