Asiya

Fafaroma ya na mai adawa da makaman Nukiliya

Fafaroma Francis a garin Nagasaki
Fafaroma Francis a garin Nagasaki REUTERS/Remo Casilli

Fafroma Francis a yayin ziyarar da ya kai kasar Japan, ya na mai bayyana takaici ganin yada wasu manyan kasashe ke ci gaba da bayyana makaman nukiliya a matsayin madogara domin kare kai daga duk wani hari ko barrazana daga abokan gaba.

Talla

A Thailand ,Fafaroma Francis ya bayyana fatan ganin kasashen Duniya sun cimma zaman lafiya,tareda kawo karshen kisan farraren hula da ake ci gaba da yi a wasu sassan.

Fafaroma Francis da ya ziyarci yankin Hiroshima, yankin da Amurka ta cilla makamin nukiliya yau da shekaru 74 da suka gabata, ya jajintawa mazauna wadanan yankuna, tareda yin kira ga manyan kasashe don ganin sun haramta kera ko kuma amfani da duk wani makamin nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI