Yemen

Saudiya na shirin sakin mayakan Huthi 200

Wasu daga cikin mayakan Huthi na Yemen
Wasu daga cikin mayakan Huthi na Yemen ©REUTERS/Khaled Abdullah

Rundunar hadaka da Saudiya ke jagoranta a Yemen, ta ce, za ta saki mayakan Huthi 200 da take tsare da su, a daidai lokacin da aka kara kaimi wajen kawo karshen rikicin da ya daidaita kasar mai fama da talauci.

Talla

Mai magana da yawun rundunar hadakar, Turki al-Maliki ya ce, za su bai wa hatta marasa lafiya damar tashi daga filin jiragen sama na birnin Sana’a domin su je su nemi magani , duk da cewa, tun shekarar 2016 aka hana jiragen fasinjoji jigila a wannan filin jiragen saman.

Tuni daya daga cikin jagororin siyasar mayakan Huthi, Mohammed Ali al-Huthi, ya yi lale marhabin da matakin da rundunar hadakar ta dauka, sannan kuma ya bukaci kawo karshen azabtar da mayakansu da ke tsare a yanzu haka.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Huthi suka sassauta kaddamar da hare-hare kan Saudiya, yayin da kuma wani babban jami’n gwamnati a birnin Riyadh ya ce, Masauratar kasar ta samar da wata ‘budaddiyar hanyar ganawa’ tsakaninta da ‘yan twayen.

Jami’in ya bayyana cewa suna goyon bayan zaman lafiya a Yemen, yana mai cewa, ko dan ba su rufe kofofinsu ga ‘yan Hurthi ba.

A ranar Jum’ar da ta gabata ne, Jakadan Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce, hare-haren da rundunar hadakar ke kaddamar sun ragu matuka a cikin makwanni biyu da suka gabata, abin da ke nuna cewa, ana samun sauyi a Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI