Bolivia

Bolivia ta nada jakada zuwa Amurka

Wasu daga cikin manoma masu goyan bayan tsohon Shugaban kasar Eva Morales
Wasu daga cikin manoma masu goyan bayan tsohon Shugaban kasar Eva Morales REUTERS/Marco Bello

Gwamnatin rikon kwarya a Bolivia, ta nada jakada zuwa Amurka karon farko a cikin shekaru 11.Wannan dai wata alama ce ta samun kusanci tsakanin Amurka da Bolivia, bayan da rikicin siyasa ya tilasta wa Evo Molares yin marabus daga mukaminsa makonni biyu da suka gabata.

Talla

Makonni biyu da suka gabata ne wakiliya a Majalisar Dattawan Bolivia ta sanar da itace sabuwar shugaban kasar bayan da Evo Morales ya ajiye shugabancin ya tsere zuwa Mexico don samun mafakar siyasa.

Jeanine Anes daga bangaren adawa ta sanar da cewa ita take kan layi a jerin masu hawa kujeran kuma za ta ci gaba da tafiyar da mulkin kasar.

Tsohon shugaba Evo Morales ya soki nadin da wakilar majalisar Dattawan ta yi cewa itace sabuwar shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.