Amurka

Kotu a Amurka ta wanke wasu mutane da aka daure shekaru 36

Zaman shara'a a kotu
Zaman shara'a a kotu GERARD JULIEN / AFP

Wata kotu a Maryland dake Amurka ta wanke wasu mutane 3 da aka daure shekaru 36 da suka gabata, saboda samun su da laifin kashe wani yaro matashi mai shekaru 14.

Talla

Rahotanni sun ce bayan samun wasu sabbin bayanai, kotun ta gamsu cewar wadannan mutane 3 basu aikata wancan laifi ba, saboda haka an sallame su su koma gida.

Ya zuwa yanzu dai ba’a bayyana diyyar da za’a biya su ba, dangane da wannan daurin da suka sha na dogon lokaci ba tare da aikata laifi ba.

Wannan sabon yanayi da aka cimma na nuna ta yadda alkalan kotu a Amurka ke zurfafa bincike don gaskiya ta bayyana dangane da wasu daga cikin hukunce-hukunce da take dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI