NATO-Turkiya

Turkiya na iya fuskantar caccaka a taron NATO

Akwai yiwuwar shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya fuskanci caccaka da takwarorinsu shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO yayin babban taron da zai fara gudana cikin makon nan a birnin London.

Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya da Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya da Emmanuel Macron na Faransa. LUDOVIC MARIN / POOL / AFP
Talla

Kwanaki kalilan gabanin taro shugaban na Turkiya da na Faransa na ci gaba da musayar zafafan kalamai, inda Macron ke zargin NATO da sakaci wajen baiwa Turkiya damar mallakar makaman kariya samfurin Rasha kirar S-400 da ke kakkaba makamai, yayinda a bangare guda Turkiya ke kokarin dakile yunkurin NATO na fara wani aikin bayar da kariya ga Poland da yankin Baltics wanda shima Faransa ke caccaka matakin.

Ka zalika tuni Turkiya ta fara gwajin makamin wanda ya janyo cecekuce tare da zargin yiwuwar ta yi amfani da shi a yakin da ta ke yanzu haka a Syria.

Taron na NATO wanda zai tabo batutuwa da dama ana ganin zai mayar da hankali sosai kan rawar da Turkiyan ke takawa a Syria duk da cewa tana iya samun cikakkiyar kariya daga Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI