Duniya
Shekaru 2010 da 2020 na a matsayin mafi fuskantar yanayin zafi a tarihin Duniya
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shekarar 2010 zuwa 2020 a matsayin mafi fuskantar yanayin zafi a tarihin Duniya, abinda ke dada nuna yadda sauyin yanayi ke shafar bil adama.
Talla
Hukumar dake kula da yanayi ta Majalisar ta bayyana yanayin zafi a wannan shekaran a matsayin wanda ya haura sama da maki guda a ma’aunin Celsius, sabanin abinda aka gani tsakanin shekarar 1850 zuwa 1900.
Wannan adadin ya sa Majalisar ta sanya shekarar 2019 a matsayin daya daga cikin shekaru 3 mafi fuskantar yanayin zafi da aka gani a Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu