Sauyin yanayi

Dubban mutane na zanga-zangar sauyin yanayi

Masu rajin kare muhalli na nuna bacin ransu kan rashin daukar matakan gaggawa domin magance dumamar yanayi a duniya
Masu rajin kare muhalli na nuna bacin ransu kan rashin daukar matakan gaggawa domin magance dumamar yanayi a duniya GABRIEL BOUYS / AFP

Dubun-dubatar masu rajin kare muhalli ne yau Juma’a ke gudanar da wani tattaki a biranen Madrid na Spain da Santiago na Chile inda suke neman daukar matakan gaggawa don kawo karshen matsalar dumamar yanayi a daidai lokacin da shugabannin duniya ke halartar taron yaki da dumamar yanayi na COP25.

Talla

Tattakin masu rajin yaki da dumamar yanayin an tsara cewa zai fi yawaita a Madrid  yayin da makamancinsa zai gudana a birnin Santiago da nufin zaburar da shugabannin duniya da ke halartar taron yaki da sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya don ganin sun dauki matakan shawo kan matsalar.

Tuni zanga-zangar ta haddasa nakasu ga taron na kwanaki 12 da ke tattaunawa kan matsalar dumamar yanayin da ta fara illa ga halittun ban-kasa.

Cikin wadanda suka tsunduma zanga-zangar ta har da Greta Thunberg, matashiyar ‘yar fafatukar yaki da dumamar yanayi da ta kaurace wa tafiye-tafiye a sararin samaniya saboda gurbatacciyar iskar da masana’antu ke haddasawa, maimakon haka ta yi tafiyar sa’o’i 10 akan ruwa daga Lisbon zuwa Madrid.

A ranar Litinin da ta gabata ne aka bude taron na yaki da dumamar yanayin na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi wa lakabi da COP25 wanda ke tattaunawa kan yadda shugabannin duniya suka gaza daukar mataki don yaki da dumamar yanayi duk da yadda aka fara ganin illarta a ban-kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI