Amurka

Pentagon ta musanta batun tura karin dakaru Golf

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta musanta rahoton da ke nuna cewa ta na shirin aikewa da karin dakaru dubu 14 yankin gabas ta tsakiya don dakile barazanar Iran ga kasashen yankin.

Talla

Cikin sanarwar ma’aikatar ta ce babu bayanan da ke kamanceceniya da rahoton jaridar Street Journal wadda ke ikirarin cewa wani babban jami’in gwamnatin kasar da bata kama sunansa ba, ya tabbatar mata yiwuwar sake aikewa da dakarun.

Rahoton na Street Journal ya bayyana cewa baya ga dakarun Amurkan akwai kuma tarin jirage da makaman yaki wanda Pentagon ke shirin girkewa a yankin na gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.