Amurka-Rasha

Amurka ta zargi Rasha da kakkabo jirginta a Libya

Jirgin yaki marar matuki samfurin Amurka.
Jirgin yaki marar matuki samfurin Amurka. Reuters

Sashen tsaron Amurka a nahiyar Afrika ya dora alhakin harbo jirgin yakinsa marar matuki can a Libya kan Rasha cikin watan jiya, jirgin da ta ce baya dauke da makami ko kuma wani abin cutarwa.

Talla

Cikin sanarwar da Amurkan ta fitar ta bukaci dawo mata da sassan jirgin wanda ta ce Rasha ce ta kakkabo shi daga sararin samaniyar birnin Tripoli.

Rasha dai na ajje da sojinta a kasar ta Libya ne don mara baya ga Khalifa Haftar wanda ke rike da iko da galibin yankunan gabashin kasar a yanzu haka kuma ya ke kokarin kwace iko da birnin Tripoli.

A cewar Janar Stephen Townsend, wanda ke jagorantar hadakar rundunonin sojin Amurka da ke nahiyar Afrika, babu tabbacin Rasha na da masaniyar jirgin na Amurka ne dalilin da ya sa ta kakkabo shi, amma akwai bukatar dawo musu da sassan jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.