Firaministan Habasha ya karbi kyautar Nobel
Wallafawa ranar:
Yau hukumar da ke bayar da kyautar Nobel ta zaman lafiya a duniya ta mika wa Firaministan Habasha Abiy Ahmed kyautar da ya samu a wannan shekarar saboda gagarumar rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasarsa da Eritrea. An gudanar da bikin mika kyautar ce a birnin Oslo.
A yayin jawabinta gabanin mika wannan kyauta ga Ahmed, shugabar Kwamitin Nobel, Berit Reiss Abdersen ta ce, an zabo shi ne saboda wasu dalilai guda uku.
"Na farko matakin da ka dauka mai muhimmanci na gina zaman lafiya tsakanin Eriterea da Habasha. Na biyu, aniyarka ta gina dimokradiya a Habasha wajen karfafa 'yanci da kuma gina ma’aikatu. Na uku an baka wannan lambar girmar ce saboda gudumawar da ka bayar wajen zaman lafiya da sasantawa a gabashi da arewa maso gabashin Afirka." in ji Andersen.
Yayin jawabinsa na karbar kyautar, Firaministan ya ce, rikici tsakanin kasashen Habasha da Eritrea ya haifar da asarar dubban rayuka.
"Lokacin yaki tsakanin Habasha da Eritrea akalla sojoji da fararen hula 100,000 suka mutu, yau muna cin moriyar shirinmu na zaman lafiya. Iyalan da suka rabu sama da shekaru 20 yau sun sake saduwa da juna, an mayar da cikakken huldar diflomasiya, an kuma mayar da sufurin jiragen sama da kuma harkokin sadarwa." In ji Ahmed.
Firaministan ya bayyana cewa, ayar Al-Kur'ani ce ta ba shi kwarin guiwa wajen samar da zama lafiya tsakanin kasashen biyu, yayin da ya bukaci kasashen duniya da su hannu da shi wajen cimma manufar shirinsa na 'Mardama' wanda aka samar da zummar gina dauwamammen zaman lafiya a arewacin Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu