Amurka

Majalisar Amurka na gab da kada kuri'a kan shirin tsige Trump

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. CHIP SOMODEVILLA / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Binciken da ka iya bada damar tsige shugaban Amurka Donald Trump daga kujerarsa, ya shiga sabon babi, inda Kwamitin Shari’a na Majalisar Dokokin Kasar a karo na 2, ya saurari bahasin da ake ganin zai kai ga fara tuhumar shugaban.

Talla

Tun a makon jiya kwamitin shari’a na majalisar dokokin Amurkan ya fara sauraron bahasin da zai bayar da damar fara tuhumar shugaba Trump.

Jim kadan bayan fara zaman kwamitin karo na 2, shugaban na Amurka ta shafinsa na Twitter ya sake nanata cewar ‘yan majalisar na democrats na yi masa bita da kulli ne kawai.

Wani lokaci nan gaba kadan ake sa ran kwamitin shari’ar majalisar dokokin kasar ta Amurka zai kada kuri’a kan daftarin zarge-zargen da aka gabatar kan shugaba Trump, idan kuma aka tabbatar da su a matsayin tuhume-tuhume, daukacin zauren majalisar dokokin ne zai kada kuri’a a kai, muddin kuma ‘yan majalisar na Democrats suka yi rinjaye, shugaba Trump zai gurfana a zauren majalisar dattijan kasar.

Mambobin Jam’iyyar Democrat na zargin Trump da karya dokokin Amurka, ta fuskokin da suka hada da, bukatar Ukraine da ta bata sunan Joe Biden da ake zaton zai kasance babban abokin hamayyarsa a zaben 2020 da ke tafe, sai kuma aikata laifin cin hanci da rashawa da kuma hana masu bincike gudanar da aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.