Birtaniya-Faransa

Birtaniya da Faransa za su ci gaba da yaki a Mali

Jiragen sama masu saukar ungulu da ke yaki da 'yan ta'adda a Mali
Jiragen sama masu saukar ungulu da ke yaki da 'yan ta'adda a Mali Souleymane AG ANARA / AFP

Kasashen Faransa da Birtaniya sun ce, za su ci gaba da yaki da ta’addanci a Mali ko da bayan ficewar Birtaniyar daga Kungiyar Tarayyar Turai don kammala kakkabe ayyukan ta’addancin da ke barazana ga tsaron kasar.

Talla

Kasashen biyu da suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar taimakekeniyar juna ta fannin tsaro a tsakaninsu cikin shekarar 2010, sun ce, ficewar Birtaniyar daga Tarayyar Turai ba za ta shafi yarjejeniyarsu.

Yayin wata ziyara da babban hafson sojin saman dakarun Birtaniya Mike Wigston tare da takwaransa na Faransa Philippe Lavigne suka kai birnin Gao na Mali, hafsoshin biyu sun ce, za su ci gaba da aiki kamar yadda suka faro a kasar ko da Birtaniya ta kammala ficewa daga EU.

A birnin na Gao, Birtaniya na da dakaru 100 da ke tallafa wa sojin Faransa dubu 4 da 500 cikin rundunar G5 Sahel a yakin da take agaza wa kasashen yankin Sahel masu fama da hare-haren ta’addanci.

Hafsoshin sojin biyu dai sun ziyarci kasashen Mali da Nijar da Chadi da kuma Burkina Faso da kuma Mauritania na yankin na Sahel da ke fuskantar barazanar tsaro ta kusan shekaru 7, inda tarin fararen hula suka hallaka yayin da wasu dubbai kuma suka kaurace wa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI