Jornalists

An kashe 'yan jaridu 49 a wannan shekarar-RSF

Wasu ma'aikata 'yan jarida a bakin aikinsu
Wasu ma'aikata 'yan jarida a bakin aikinsu FRANCOIS NASCIMBENI / AFP

Kungiyar kare 'yan jaridu ta duniya ta ce, 'yan jaridu 49 aka kashe a cikin wannan shekara ta 2019, adadin da  shi ne mafi karanci a cikin shekaru 16.

Talla

Kungiyar da ke da cibiya a birnin Paris na Faransa, ta bayyana aikin jarida a matsayin mafi hadari, ganin yadda ma’aikata ke rasa rayukansu musamman a kasashen da ke fama da tashin hankali irinsu Yemen da Syria da Afghanistan.

Alkaluman kungiyar sun nuna cewa, akalla 'yan jaridu 80 ke rasa rayukansu a kowacce shekara a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, 'yan jaridu 389 aka daure a cikin wannan shekara, adadin da ya karu da kashi 12 akan na shekarar 2018, kuma kasashen China da Masar da Saudi Arabia ne ke kan gaba wajen garkame mafi yawan 'yan jaridun.

Kungiyar ta ce, ya zuwa yanzu 'yan jaridu 57 aka yi garkuwa da su a fadin duniya, kuma akasarinsu sun fito ne daga kasashen Syria da Yemen da Iraqi da kuma Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI