Amurka- Rasha

Rasha ta kaddamar da shu'umin na'urarta

Na'urar za ta rika kakkabo makamai masu linzami
Na'urar za ta rika kakkabo makamai masu linzami Tech. Sgt. Kamaile Casillas/Pacific Air Forces/DVIDS/Handout via

Kasar Rasha ta yaye hijabin na’urarta ta kakkabo makamai masu linzami wadda ta adana a sararin samaniya a daidai lokacin da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da shirin shugaba Donald Trump na kafa sabuwar rundunar sojin kasar a sararin samaniyar.

Talla

Sabuwar na’urar ta Rasha wadda aka yi wa lakabi da Kupol ko kuma Dome, an kera ta ne domin gano hare-haren makamai masu linzami tare da bin sahunsu har zuwa wurin da za su yi dirar karshe.

Kawo yanzu babu cikakkiyar masaniya game da hakikanin hade-haden da aka yi wajen kera wannan shu’umin na’ura ta Kupol wadda tsayuwarta ta yi kama da irin tsayuwar na’urar bincike ta SBIRS da Amurka ta ajiye a sararin samaniyar.

Babban Hafsan hafsoshin rundunar sojin Rasha, Janar Valery Gerasimov ya ce, sabuwar na’urar ta karfafa karfin kasar wajen mallaka da kuma gano makamai masu linzami da aka kaddamar da hare-harensu.

Kalaman Janar Gerasimov na zuwa ne kwana guda da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da Dala biliyan 738 a matsayin kudaden da za a kashe domin kafa sabuwar rundunar sojin kasar a sararin samaniya, rundunar da za ta kasance karkashin kulawar bangaren sojin saman Amurka.

Tun a shekarar 2015 Rasha ta samar da irin wannan runduna ta sararin samaniya wadda ke karkashin kulawar sojin samanta.

Rasha ta dade tana zargin Amurka da yunkurin amfani da dakarunta wajen addabar sararin subhana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI