Amurka ta laftawa kamfanin ginin bututun gas din Rasha takunkumi
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da kakaba wasu takunkuman karya tattalin arziki kan kamfanonin da ke aikin ginin bututun iskar gas daga Rasha zuwa Jamus, takunkuman da Turai ta jima tana fafatukar ganin amurka bata sanya ba.
Sabbin takunkuman dai kai tsaye za su sake raa dangantakar da ke tsakanin Rashan da takwarorinta kasashen Turai dai dai lokacin da wasu kasashen ciki har da Faransa ke kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu da Kremlin.
Yanzu haka dai manyan kamfanonin Turai biyu da ke aikin ginin butun ta karkashin tekun Baltic da kudinsa ya kai dala biliyan 11 za su fuskanci takunkuman daga Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu