Macron-Faransa

Mulkin mallakar Turawa a Afrika babban kuskure ne- Macron

Shugaba Emmanuel Macron a ganawarshi da wasu shugabannin kabilu a Ivory Coast.
Shugaba Emmanuel Macron a ganawarshi da wasu shugabannin kabilu a Ivory Coast. REUTERS/Thierry Gouegnon

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana mulkin mallakar da turawa suka yiwa kasashen Afrika a matsayin mummunan kuskuren da ya haddasa tarin matsaloli a nahiyar.

Talla

Yayin ziyarar da shugaban ke ci gaba da yi a Ivory Coast don gudanar da bukukuwan Kirsimeti da Sojinsa dubu guda da ke Abidjan, ya ce lokaci ya yi daya kamata a manta baya don gujewa sake fuskantar kura-kurai.

Cikin kalaman na Macron ya ce bai fito daga tsatson da ke goyon bayan mulkin mallaka ba, yana mai cewa nahiyar Afrika yanki ne na sabbin jini da kashi 3 cikin hudun al’ummarsa basu san mulkin mallaka ba, don haka bai kamata matasa su taso da akidar tunowa da wancan yanayi a zukatansu ba.

Kalaman na Macron dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Faransa ke ci gaba da fuskantar kyama daga kasashen da ta yiwa mulkin mallaka, ciki har da Jamhuriyyar Nijar kasar da a baya-bayan nan suka rika gudanar da mabanbantan zanga-zangar kin jinin Faransawa, musamman bayan kisan Sojinsu 71.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.