An balle hancin mutun-mutumin Ibrahimovich a Sweden

Wasu da ba a san ko su waye ba, sun bantare hancin mutun-mutumin Zlatan Ibrahimovic, dake mashigin filin wasan Malmo a kasar Sweden.

Zlatan Ibrahimovic sanye da kayan wasan Manchester United
Zlatan Ibrahimovic sanye da kayan wasan Manchester United Adam Yates/Reuters
Talla

Wannan dai na amatsayin fushin wasu ‘yan kasar sakamakon sanarwar dan wasan mai shekaru 38, na cewar ya sayi hannun jari a wata kungiyar hamayya.

Tuni Wanda ya gina mutun-mutumin dan wasan, Peter Linde ya nuna batcin ransa, inda ya yi kira ga mutane da su daina lalata masa aikin da ya yi.

Zlatan Ibrahimovich wanda ya kwashe fiye da shekaru 20 yana wa club dinsa na Malmo wasa, ya yi wasanni a kungiyoyin irinsu Ajax da Juventus da Inter Milan, da Ac Milan da Barcelona da Paris St Germain da Manchester United, na neman wata kungiya, bayan da ya bar LA Galaxy ta Amurka a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI