Saudiya

Saudiya za ta kashe mutanen da suka hallaka Khashoggi

Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi DR

Wata Kotun Saudiya ta zartas da hukuncin kisa kan mutane biyar, yayin da ta garkame uku a gidan yari bayan ta same su da hannu a kisan dan jaridar kasar, Jamal Khahoggi a bara.

Talla

Marigayi Jamal Khashoggi da ya shahara wajen sukar manufofin gwamnatin Saudiya, an kashe shi ne a cikin ofishin jakadancin Saudiyar da ke birnin Santanbul na Turkiya.

Mahukuntan Saudiya sun bayyana kisan Khashoggi a matsayin mugunta, yayin da suka tuhumi mutane 11 da ake zargi.

A cikin watan Yulin da ya gabaata, wata babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya, Agnes Callamard ta ce, akwai kwararan shaidu da ke bada damar zurfafa binciken manyan hukumomin Saudiya da suka hada da Yarima mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman da ake zargi da hannu a kisan.

Sai dai Yariman ya musanta hannu kafin a cikin watan Oktoba ya bayyana cewa, ya dauki cikakken alhaki a matsayinsa na jagora a Saudiya musamman ganin cewa, wasu mutane da ke yi wa gwamnatin kasar aiki ne suka aikata kisan.

A ranar 2 ga watan Oktoban bara aka ga Khashoggi mai shekaru 59 kuma marubuci a Jaridar Washington Post ta Amurka, na shiga ofishin jaladancin Saudiya a Santanbul da nufin karbo wasu takardun shirye-sjiryen aurensa da budurwarsa, amma tun daga wancan lokacin ba sake jin duriyarsa ba.

Daga bisani wasu bayanai sun ce, an yi gunduwa- gunduwa da namansa bayan tawagar mutun 15 ta mahukre shi har lahira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI