Iran-Amurka

Mutane dubu 1 da 500 ne suka mutu a zanga-zangar Iran- Amurka

Dandazon masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran.
Dandazon masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran. ATTA KENARE / AFP

Kasar Amurka ta tabbatar da sahihancin rohoton baya-bayan nan da ke bayyana adadin mutanen da jami’an tsaron Iran suka kashe yayin zanga-zangar kasar ta kin jinin Gwamnati cikin watan Nuwamba daya gabata zuwa mutum dubu 1 da dari 5.

Talla

Cikin sanarwar da Amurka ta fitar yau Talata ta kafa hujja da bayanan da ta samu ta hannun wani babban jami’in Iran da bata bayyana sunanshi ba, wanda ta ce ya tabbatar mata da adadin mutanen ya tasamma dubu 1 da 500.

Cikin rahoton da shafin Reuters na Birtaniya ya wallafa ya bayyana cewa bayanai daga ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Iran ya nuna cikin mutanen da aka kashe yayin zanga-zangar ta watan jiya har da matasa 17 baya ga mata 400 tare kuma da su kansu jami’an tsraon da suka rasa rayukansu a gangamin.

Cikin sakon Twitter da hukumar tsaron sirri a Amurkan ta fitar ta ruwaito Brian Hook babban jami’in Amurka na musamman a Iran na cewa rahoton Reuters ne ya bayyana hakikanin mutanen da suka mutu a zanga-zangar yana mai cewa nauyi ne kan kasashen duniya wajen ganin an biya mutanen hakkinsu.

Adadin da Reuters ta wallafa na mutanen da aka kashe a zanga-zangar kin jinin gwamnatin a Iran dai ya ninninka adadin da kungiyar Amnesty International ta bayyana tun da farko da ta ce jami’an tsaron Iran sun kashe masu zanga-zanga 304 tun bayan barkewar zanga-zangar a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Dama dai tun a ranar 5 ga watan nan Brian Hook y ace akwai hujjoji da ke nuna cewa mutanen da jami’an tsraon Iran suka hallaka yayin zanga-zangar yah aura dubu guda, zanga-zangar da ta samo asali sanadiyyar matsin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI