Duniya

Miliyoyin al'ummar Kirista sun fara bikin Kirsimeti a sassan duniya

Wasu mabiya addinin Kirista yayin addu'ar Kirssimeti.
Wasu mabiya addinin Kirista yayin addu'ar Kirssimeti. REUTERS/Eric Gaillard

Mabiya addinin Kirista daga sassa daban-daban na duniya, na ci gaba da shagulgulan bikin Kirsimeti a yau Laraba da ke matsayin ranar tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.

Talla

Shugaban Darikar Katlika na duniya Fafaroma Francis a sakon taya murnar zagayowar ranar da ya aikewa miliyoyin mabiyansa, ya bukaci daukar matakan gyara a munanan dabi’un da al’umma ke aikatawa a ban kasa.

Yayin jawabinsa gaban taron jama’ar da suka halarci sujjadar Kirsimati a fadarsa ta Vatican ya ce duk da munanan dabi’u da zunufan da al’umma ke aikatawa ubangiji a shirye ya ke ya yafe musu matukar suka mika kai gareshi.

Shugaban na Katlika, ya kuma koka da yadda cin zarfin mata ke ci gaba da ta’azzara ciki har da wanda ake tuhumar manyan limaman majami’a da aikawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.