Indonesia

An yi addu'ar tunawa da mamatan tsunami

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa iyalansu a ibtila'in tsunami a Indonesia
Wasu daga cikin mutanen da suka rasa iyalansu a ibtila'in tsunami a Indonesia REUTERS/Beawiharta

Dubban al’ummar Indonesia sun yi dandazo a manyan kaburburan da ke lardin Aceh domin tunawa da iyalansu da suka rasa rayukansu a gagarumin ibtila’in ambaliyar ruwan tsunami da ya afaka wa kasar shekaru 15 da suka gabata.

Talla

Ana kallon wanan ibtila’in wanda ya auku a shekarar 2004, a matsayin daya daga cikin munanan bala’o’i da suka cika da bil’adama a tarihi, yayin da mutane akalla dubu 170 suka rasa rayukansu a lardin Aceh na Indonesia kadai.

Iyalan mamatan sun yi addu’o’in tunawa da su tare da baza furanni a kaburburan da aka binne su a daidai lokacin da aka cika shekaru 15 da aukuwar ambaliyar ta tsunami.

Nurhayati wadda ta rasa ‘yarta mai shekaru 17 a ibtila’in na tsunami, ta ce, har yanzu tana kaduwa matuka a duk lokacin da ta yi ido biyu da ruwan teku saboda tana jin tamkar wani ibtila’in tsunamin zai barke.

A ranar 26 ga watan Disamban shekarar 2004 ne, ambaliyar karkashin ruwan mai karfin maki 9.1 ta afka wa Indonesia mai yawan al’ummar Musulmi, lamarin da ya haddasa igiyar tsunami wadda ta kashe wasu karin mutane dubu 50 a kasashen da ke gabar tekun India da suka hada da Somalia a Afrika.

Duk da cewa, an kwashe tsawon shekaru da aukuwar wannan al’amari, amma har yanzu ana gano gawarwaki jifa-jifa , inda ko a bara aka gano gawarwakin gomman mutane a wata farfajiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI