Iran-Rasha-China

Iran, Rasha da China sun fara atisayen sojin ruwa na hadin gwiwa

jiragen yakin Rasha da Iran.
jiragen yakin Rasha da Iran. Royal Navy/Handout via REUTERS

Kasashen Iran China da kuma Rasha sun fara wani atisayen sojin ruwa na hadin gwiwa tsakanin dakarun sojinsu a tekun India da na Oman, atisayen da ke zuwa dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Iran da Amurka tun bayan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Talla

A cikin jawabin shugaban dakarun Sojin ruwan Iran, Real Admiral Gholamreza Tahani, da ya gabatar kai tsaye ta gidan talabijin din kasar, ya ce atisayen hadakar ba komi ya ke nufi ba, face hadin kai da wanzar da zaman lafiya baya ga tsaron kasashen 3.

A cewar Gholamreza sabon kawancen tsakanin sojin ruwan kasashen na Iran Rasha da kuma China zai karfafa dangantar da ke tsakaninsu baya ga bayar da cikakkiyar kariya ga tsaron ruwansu.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni manyan jiragen ruwan Rasha na yaki suka isa gabar ruwan kudancin Iran, yayinda kowanne lokaci daga yanzu ake tsammanin isowar jiragen China ko da yake da tuni aka fara wani bangaren na atisayen tun a safiyar yau Juma’a.

Kwamanda Gholamreza ya bayyana cewa baya ga tsaro da atisayen zai baiwa kasashen 3 zai kuma taimaka wajen bunkasa cinikayyarsu.

Sabon hadakar Sojin na matsayin kishiya ga rundunar sojin ruwan Amurka da ta fadada atisayenta a tekunan yankin na Gulf don bayar da tsaro ga kawayenta na Saudiya da Hadaddiyar daular Larabawa tun bayan harin ‘yan tawayen Houthi kan matatun man Saudiya na Aramco mafi girma a duniya, harin da Amurka ke zargin Iran da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI