Amurka-Iraq

Farmakin Amurka ya kashe mayakan Hezbollah

Farmakin da Amurka ta kaddamar da jiragen yakinta kan kungiyar da ke samun goyon bayan Iran, ya kashe akalla mayaka 25 a Iraqi, lamarin da ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya tsakanin mahukuntan Tehran da Washington.

Amurka ta bayyana farmakinta kan dakarun Hezbollah a matsayin nasara
Amurka ta bayyana farmakinta kan dakarun Hezbollah a matsayin nasara REUTERS/US Navy/
Talla

A cikin daren da ya gabata ne, jiragen Amurka suka kaddamar da hare-hare kan sansanonin kungiyar Hezbollah wadda ke zama reshen Hashed al-Shaabi kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.

Baya ga mutane 25 da suka rasa rayukansu, har ila yau, akwai 51 da suka jikkata da suka hada da Kwamandojin mayakan, yayin da ake sa ran karuwar alkaluman nan gaba.

Kungiyar Hashed al-Shaabi ta ce, har yanzu tana kan gudanar da aikin zakulo mutane daga karkashin buraguzan sansanin da ke kusa da yankin Al-Qaim wanda ke kan iyakar Iraqi da Syria.

Ma’aikatar Harkoki Wajen Iran ta ce, kasar Amurka ta nuna kudirinta karara na goyon bayan ayyuakan ta’addanci, tare da keta ‘yancin kasashe, lura da wannan farmakin da ta kaddamar a Iraqin.

Ita kuwa Ma’aikatar Tsaron Amurka ta bakin Sakatarenta, Mark Esper, ta bayyana farmakin a matsayin nasara, yayin da kasar Bahrain da ke zama aminiya ga Amurka, ta yi lale marhabin da harin.

Ana kallon farmakin a matsayin ramuwar gayya kan jerin hare-haren da aka kai wa wasu manufofin Amurka a Iraqi da suka hada da harin da ya kashe wani Ba’amurke dan kwangila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI