Australia

Gobarar daji ta kori dubban mutane a Australia

An tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 a sanadiyar gobarar dajin Autsralia
An tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 a sanadiyar gobarar dajin Autsralia PETER PARKS / AFP

Ma’aikatan kwana-kwana da baki masu yawon bude ido a Australia na tsarewa daga yankin kudu maso yammacin kasar sakamakon tsananin zafi a daidai lokacin da ake fama da ibtila’in wutar daji a kasar.

Talla

Mahukunta sun ce, kimanin mutane dubu 30 suka bukaci a tsirar da su daga yankin Gippsland, da ke kudu maso yammacin kasar.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara a yankin Ben Rankin ya ce, yanayin zafin da yankin ke fuskanta ya wuce kima, abin da ke barazana ga lafiyar ‘yan yawon bude ido da ma’aikatan kwana-kwana.

Sakamakon yadda wutar dajin ke kara bazuwa da kuma tsananin zafi da ta haifar, yanzu haka daruruwan jami’an kwana-kwana sun janye daga yankin na Gippsland da akalla kilomita dubu 1 daga gobarar da ake danganta ta da canjin yanayi.

Kimanin kadada miliyan uku, wato kwatankwacin girman kasar Belgium ya kone kurmus a yankin a sanadiyar wannan gobara da ta hallaka mutane akalla 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI