Amurka-Iraq

Trump ya ce Iran za ta girbi mummunan sakamako

Wasu daga cikin masu zanga-zangar a harabar ofishin jakadancin Amurka dake Iraqi
Wasu daga cikin masu zanga-zangar a harabar ofishin jakadancin Amurka dake Iraqi REUTERS/Wissm al-Okili

Shugaba Donald Trump ya ce Iran za ta girbi mummunan sakamako biyo bayan da harin da dubban matasa suka kai wa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagadaza tare da kona wani bangare na ofishin a jiya talata.

Talla

A sakon da ya fitar a shafinsa na Twitter shugaba Trump ya ce ‘’wannan ba wai gargadi ba ne barazana ce’’ ga kasar ta Iran. To sai dai ya ce ba ya fatan barkewar yaki tsakanin kasashen biyu.

Sakataren tsaron Amurka Mark Esper, ya ce kasar za ta tura karin sojoji 750 cikin gaggawa zuwa yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan wannan lamari da ya faru a birnin Bagadaza, yayin da alkaluma ke tabbatar da cewa akwai wasu sojoji sama da dubu biyar a yankin.

Gwamnatin Iran ta musanta cewa tana da hannu a tarzomar da aka yi a zagayen ofishin jadakancin na Amurka, to sai dai kasar ta ce tana cikin shirin maryar da martani matukar Amurka ta yi gigin kai ma ta hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI