Turkiya-Libya

Majalisar Turkiya na kada kuri'ar tura dakaru Libya

Wani ayarin motocin sojojin Turkiya
Wani ayarin motocin sojojin Turkiya REUTERS

A yau Alhamis Majalisar Dokokin Turkiyya ke bayyana matsayinta dangane da bukatar shugaba Racep Tayyip Erdogan da ke neman izinin tura sojoji zuwa Libya don kare gwamnatin birnin Tripoli.

Talla

A watan nuwamban da ya gabata ne shugaba Erdogan ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da Firaministan Libya Fayez el-Sarraj don bai wa gwamnatinsa kariya daga hare-haren dakarun Khalifa Haftar.

Turkiyya ta ce, shiga yakin ya zama wajibi, domin hana Libya ci gaba da kasancewa tungar ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifufuka, abin da ke zama babbar barazana ga tsaron kasashen yankin baki daya.

Ana dari-darin cewa, shigar dakarun Turkiya cikin Libya ka tsananta yakin da kasar ta dauki tsawon shekaru tana fama da shi, abin da ya sa jam’iyyar adawa a Majalisar Dokokin Turkiyar ta ce, za ta kada kuri’ar kin goyon bayan tura dakarun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.