Iran bazata mikawa Amurka bakin akwatin Jirgin Ukraine da ya yi hatsari ba
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ma’aikatar da ke kula da sufurin jiragen sama a Iran ta ce ba ta da niyyar baiwa Amurka bakar akwatin jirgin Ukraine kirar Boeing 737 da ya yi hadari cikin daren jiya Talata tare da hallaka ilahirin fasinjan da ke cikinsa 176.
Shugaban sashen ma’aikatar Ali Abedzadeh ya ce ko kadan baza su damkawa kamfanin na Boeing da ke Amurka ko kuma mahukuntan kasar bakar akwatin jirgin ba, ko da dai Iran ba ta fayyace inda za ta aike da bakar akwatin don gudanar da binciken ba.
Jirgin saman kasar Ukraine dauke da fasinjoji 170 din ya yi hatsari ne a kasar Iran mintuna kadan bayan tashinsa a birnin Tehran.
Bayanai sun ce jirgin kirar Boeing 737 mallakin kasar Ukraine ya tashi daga Tehran ne domin zuwa birnin Kiev,inda Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya tabbatar da mutuwar ilahirin fasinjojin dake cikin wannan jirgi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu