Iran -Amurka-Iraqi

Iran ta mayar da martani farko kan Amurka

Sansanin sojin Amurka da Iran ta kaiwa hari a Iraqi
Sansanin sojin Amurka da Iran ta kaiwa hari a Iraqi RFI

Kwana daya bayan kammala jana’izar janar Qasem Soleimani, a cikin daren a ya gabata rundunar sojin Iran ta mayar da martani na farko kan kasar Amurka, ta hanyar harba rokoki fiye da 12 a kan sansanonin kasar biyu da ke cikin Iraki.

Talla

Wasu daga cikin makamai masu linzamen da Iran ta harba sun fada ne a kan barikin sojin Aïnal-Assad, tazarar kilomita 230 a yammacin birnin Bagadaza, barkin da Donald Trump ya ziyarta don ganawa da dakarun Amurka a watan disambar shekara ta 2018, yayin da sauran makaman suka fada a barikin sojin Erbil da ke gabashin kasar.

Sanarwar da ta fitar jim kadan bayan wadannan hare-hare, rundunar kare juyin juya halin musuluncin kasar ta Iran ta ce ta shirya tsaf domin yi fito na fito da Amurka, tare da yin barazanar kai irin wadannan hare-hare a kan kasar Isra’ila, yayin da ta ce duk wata kasa da Amurka za ta yi amfani da ita don kai mata Iran farmaki ita ma za ta iya fuskantar mummunan martani.

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta tabbatar da kai hare-haren, inda ta ce yanzu haka ana ci gaba da tantance irin illolin suka haddasa, yayin da wani lokaci a yau shugaban Donald Trump zai gabatar da jawabi ga al’ummar kasar ta Amurka.

Lura da halin da ake ciki, Amurka ta bukaci jiragenta da jigilar fasinjoji da su kaurace wa sararin samaniyar yankin gabas ta Tsakiya baki daya.

Kasuwannin hannayen jarin kasashen Asiya a yau sun bude a cikin yanayi na firgita, yayin da tuni farashin man fetur ya tashi da akalla 4,5% a yankin na Asiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI