Iran -Amurka-Iraqi

Canada ta zargi Iran da harbo jirgin fasinja na Ukraine

Hatsarin jirgin fasinjan kasar Ukraine a Tehran na kasar Iran
Hatsarin jirgin fasinjan kasar Ukraine a Tehran na kasar Iran Nazanin Tabatabaee/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS

Justin Trudeau Fira Ministan Canada ya ce bayanan da masu bincike daban daban sun nuna cewar Iran ce ta yi kuskuren kakkabo jirgin Fasinja mallakin Ukraine da ya rikito a wajen birnin Tehran.

Talla

Kafin jawabin Firaministan na Canada, sai da masu bincike daga Ukraine suka zayyana yiwuwar harbo jirgin saman da makami mai linzami, ko kuma lalacewar injinsa, a matsayin dalilan da suka haddasa hadarin.

Fasinjoji 176 dake cikin jirgin na Ukraine suka halaka, bayan da jirgin ya fado jim kadan da tashinsa a ranar laraba, a dai dai lokacin da Iran ta harba makamai masu linzami har kashi 22 kan sansanonin sojin Amurka dake birnin Bagadaza a Iraqi.

Masu bincike da wasu shaidun gani da ido dai sun bayyana cewar, jirgin fasinjan ya kama da wuta tun kafin ya kai ga fadowa, sakamakon samunsa da daya daga cikin makamai masu linzamin da Iran ta harba kan dakarun Amurka yayi.

63 daga cikin fasinjojin 176 da suka halaka ‘yan kasar Canada ne, sai kuma ‘yan Ukraine 11.

Iran ta bukaci wasu kasashe da su aike da masu bincike da zasu aiki da jami'am ta dangane da wannan hatsari na jirgin fasinjan Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI