Iraqi-Amurka-Ukraine-Canada

Iran ta amsa laifin harbo Jirgin Ukraine bisa kuskure

Masu bincike biyo bayan fashewar jirgin fasijan kasar Ukraine a Tehran
Masu bincike biyo bayan fashewar jirgin fasijan kasar Ukraine a Tehran © Nazanin Tabatabaee/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS

Bayan share dan gajeren lokaci ana caccar baka dangane da batun harbor jirgin fasijan Ukraine aTehran, kasar Iran ta amsa cewa bisa kuskure ne rundunar tsaron kasar ta kakkabo jirgin fasinjan kasar Ukraine yan lokuta da cirawar sa daga filin tashi dama saukar jiragen saman birnin Tehran.

Talla

Kasashen Canada da Ukraine sun bukaci a gurfanar da sojojin dake da hannu a batun harbo jirgin fasijan Ukraine tareda samar da hanyoyin biyan diya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukan su .

Mutane 176 ne suka rasa rayukan a wannan hatsari da ya hauku a Tehran.

Ministan harakokin wajen kasar ta Iran Javad Zarif ya roki iyalen mamatan, tareda neman gafarar jama’a biyo bayan wannan kuskure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.