Philippines

Iftila'in dutse mai aman wuta a Philippines ya ta'azzara

Dutsen Taal mai aman wuta a Philippines
Dutsen Taal mai aman wuta a Philippines Jon Patrick Laurence Yen via REUTERS

Wani dutse mai aman wuta a Philippines ya fara fitar da narkakkiyar laka, a yayin da hukumomin kasar suka gargadi cewa, za a dauki tsawon sa’o’i ko kuma kwanaki ana fama da wannan ibtila’in da ka iya ta’azzara.

Talla

A safiyar wannan Litinin ne dutsen Taal wanda ke da tazarar kilomita 70 daga kudancin babban birnin Manila na kasar Philippine ya fara fitar da narkekken dutse.

Wannan na zuwa ne bayan dutsen ya fitar da tarin toka a jiya Lahadi, lamarin da ya tilasta wa hukumomin kasar kwashe mutane kimanin dubu 8 daga yankin.

Dutsen Taal shi ne na biyu mafi girma daga cikin jerin duwatsu masu aman wuta a Philippines.

Kodayake dutsen wanda ke zama a tsakiyar wani tsibiri, na daga cikin kananan duwatsu masu aman wuta a duniya, inda a tsawon shekaru 450, ya yi aman wuta sau 34 kacal.

Hukuomin kasar sun gargadi samun ambaliyar ruwan tsunami wadda ka iya barkewa a sanadiyar tarwatsewar buraguzan dutsen na Taal, abin da zai hifar da igiyar ruwa a cewarsu.

Alkaluma sun nuna cewa, a jumulce, an samu girgizar kasa har sau 75 a yankin na Taal, amma 32 daga cikin girgizar kasar sun yi muni.

Tuni shugaban kasar, Rodrigo Duterte ya dakatar da gudanar da ayyukan gwamnati a birnin Manila, sannan kuma ya bayar da umarnin rufe makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.